ha_obs/content/41.md

2.3 KiB

41. Allah ya Tada Yesu daga Matattu

OBS Image

Bayan sojajin sun gicciye Yesu, sai shugabannnin Yahudawa marasa bangaskiya suka cewa Bilatus, ''Wannan makaryacin, Yesu, ya ce zai tashi daga matattu bayan kwana uku. Don haka lallai ne wani yayi tsaron kabarin, domin a tabbata cewa almajiran sa ba su saci gangar jikinsa ba, sa'annan su ce ya tashi daga matattu.''

OBS Image

Bilatus yace, ''Ku dauki wassu sojoji kuje ku tsare kabarin gwargwadon iyawarku.'' Sai suka sa hatimi a kan dutsen da ke kofar kabarin da kuma sojoji don su tabbata ba wanda zai iya satar gangar jikin.

OBS Image

Bayan ranar da aka binne Yesu, ranar asabar ce, kuma ba a yardar wa Yahudawa suje kabari a ranar ba. Sai da sassafe bayan asabar, mata da yawa suka yi shiri suje kabarin Yesu, domin su kara zuba turare a gangar jikin sa.

OBS Image

Nan da nan, sai aka yi babbar girgizar kasa. Wani mala'ika mai haske kamar walkiya ya bayyana daga sama.Ya mirgina dutsen dake rufe kofar kabarin gefe guda, ya zauna akai. Sojojin dake tsaron kabarin suka firgita, suka fadi kasa kamar matattun mutane.

OBS Image

Sa'anda matan suka isa kabarin, sai mala'ikan yace masu, "Kada kuji tsoro. Yesu baya nan. Ya tashi daga matattu kamar yadda yace zai yi! Ku duba cikin kabarin ku gani.'' Matan suka duba cikin kabarin inda aka kwantar da jikin Yesu. Babu jikin a wurin!

OBS Image

Sa'annan mala'ikan yace wa matan, ''Kuje ku gaya wa almajiran, 'Yesu ya tashi daga matattu kuma zai riga ku zuwa Galili.'''

OBS Image

Matan suka cika da tsoro da farin ciki. Suka ruga domin su fada wa almajiran wannan labari mai dadi.

OBS Image

Yayin da matan suke hanyar zuwa su fada wa almajiran labarin nan mai dadi, sai Yesu ya bayyana a gare su, sai suka yi masa sujada. Yesu ya ce, ''Kada ku ji tsoro. Ku je ku gaya wa almajiraina su tafi Galili. Zasu gan ni a can.''

Labari a Littafi Mai Tsarki daga: Matta 27:62-28:15; Markus 16:1-11; Luka 24:1-12; Yahaya 20:1-18