ha_obs/content/21.md

5.0 KiB

21. Allah ya yi Alkawarin Almasihu

OBS Image

Tun daga farko, Allah ya yi shirin aiko da Almasihu. Alkawarin farko na Almasihu ya zo ga Adamu da Hauwa'u. Allah yayi alkawari cewa za'a haifi zuri'ar Hawa'u wanda zai kuje kan macijin. Macijin da ya yaudari Hauwa'u Shaidan ne. Ma'anar alkawarin shine Almasihu zai yi nasara akan Shaidan gaba daya.

OBS Image

Allah yayi wa Ibrahim Alkawari cewa ta wurin sa duk kabilun mutanen duniya zasu sami albarka. Wannan Alkawari zai cika yayinda Almasihu zai zo nan gaba. Zai ba wa mutane na dukkan kabilun duniya damar su sami ceto.

OBS Image

Allah ya yi wa Musa alkawari cewa nan gaba zai tada wani annabi kamar Musa. Wannan wani alkawari ne kuma game da Almasihu wanda zai zo wani lokaci nan gaba.

OBS Image

Allah yayi wa Sarki Dauda alkawari cewa daya daga cikin zuriyarsa zai yi mulki kamar sarki a bisa mutanen Allah har abada. Wannan ya nuna cewa Almasihun zai zama daya daga cikin zuriyar Dauda.

OBS Image

Ta wurin annabi Irimiya, Allah yayi alkawari cewa zai yi sabon Wa'adi, amma ba kamar Wa'adin da yayi da Isra'ila a Sina'i ba. A wannan Sabon Wa'adi, Allah zai rubuta shari'arsa a zukatan mutane, mutanen kuma zasu san Allah da kansu, zasu zama jama'arsa, Allah kuma zai gafarta masu zunuban su. Almasihu ne zai fara Sabon Wa'adi.

OBS Image

Annabawan Allah kuma sun ce Almasihun zai zama annabi, firist, da kuma sarki. Annabi mutum ne da ke jin kalmomin Allah sa'annan ya sanar da kalmomin Allah ga mutane. Almasihu wanda Allah yayi alkawari zai aiko zai zama cikakken annabi.

OBS Image

Firistocin Isra'ila sun mika hadayu ga Allah a madadin mutane a maimakon hukuncin zunubansu. Firistoci kuma sun yi addu'a ga Allah domin mutane. Almasihu zai zama cikakken babban firist wanda zai mika kansa cikakken hadaya ga Allah.

OBS Image

Sarki mutum ne mai sarauta akan mulki yana kuma shar'ianta mutane. Almasihu zai zama cikakken sarki da zai zauna akan kursiyin kakan kakaninsa Dauda. Zai yi mulki bisa duniya duka har abada, kuma a koyaushe zai yi shari'ar gaskiya ya kuma yanke shawara da adalci.

OBS Image

Annabawan Allah sun yi anabcin wassu abubuwa da yawa game da Almasihu. Annabi Malakai yayi anabcin cewa wani babban annabi zai zo kafin zuwan Almasihu. Annabi Ishaya yayi anabci cewa za'a haifi Almasihu ta wurin budurwa. Annabi Mika yace za'a haife shi cikin birnin Baitalami.

OBS Image

Annabi Ishaya ya ce Almasihu zai zauna a Galili, ya ta'azantar da mutane masu karyayyar zuciya, yayi shelar yanci ga daurarru da kuma saki ga wadanda ke kurkuku. Ya kuma yi annabci cewa Almasihun zai warkar da mutane masu ciwo da wadanda ba sa iya ji, gani, magana, ko tafiya.

OBS Image

Annabi Ishaya kuma yayi annabci cewa za'a tsani Almasihu ba dalili a kuma ki shi. Wadansu annabawa sun yi annabci cewa wadanda zasu kashe Almasihu zasu yi kuri'a akan tufafinsa sa'annnan kuma wani amini zai ci amanarsa. Annabi Zakariya yayi annabci cewa za'a biya aminin tsabar azurfa talatin a matsayin hakin cin amanar Almasihu.

OBS Image

Annabawan kuma sun fadi yadda Almasihu zai mutu. Ishaya yayi annabci cewa mutune zasu tofa masa yawu, suyi masa ba'a, su kuma doddoki Almasihun. Za su soke shi zai kuma mutu cikin azaba mai tsanani da radaddi, ko da shike bai yi wani laifi ba.

OBS Image

Annabawan kuma sun ce Almasihun zai zama cikakke, marar zunubi. Zai mutu domin ya dauki hukunci na zunuban wassu mutane. Hukuncinsa zai kawo salama tsakanin Allah da mutane.Saboda wanan dalili, nufin Allah ne ya kuje Almasihu.

OBS Image

Annabawan sun yi annabci cewa Almasihun zai mutu, Allah Kuma zai tashe shi daga matattu. Ta wurin mutuwar Almasihu da tashinsa, Allah zai kammala shirinsa na ceton masu zunubi, ya kuma fara Sabon Wa'adin.

OBS Image

Allah ya bayyana wa annabawa abubuwa da yawa game da Almasihu, amma Almasihu bai zo a lokacin da ko daya daga cikin annabawan nan na nan ba. Fiye da shekaru 400 bayan an bada annabci na karshe, a cikar lokaci daidai, Allah zai aiko da Almasihu cikin duniya.

Labari a Littafi Mai Tsarki Daga: Farawa 3:15; 12:1-3; Maimaitawar Shari'a 18:15; 2 Sama'ila 7; Irimiya 31; Ishaya 59:16; Daniyel 7; Malakai 4: 5; Ishaya 7:14; Mika 5: 2; Ishaya 9:1-7; 35:3-5; 61;53; Zabura 22:18; 35:19; 69:4; 41:9; Zakariya 11:12-13; Ishaya 50:6; Zabura 16:10-11